IQNA

Sakon ta'aziyyar jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran  bayan shahadar Ismail Haniyya:

Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta shirya fage da za ta  fuskanci azabtarwa mai tsanani

15:49 - July 31, 2024
1
Lambar Labari: 3491611
IQNA - A cikin sakonsa na cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi ta'aziyyar shahadar babban mujahidin Isma'il Haniyyah shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas inda ya ce: Hukumar 'yan ta'adda ta Sahayoniyya ta shirya tsatsauran hukunci  ita kanta da wannan aiki, da ta aikata a cikin yankin Jamhuriyar Musulunci Iran , kuma martini kan hakan wajibi ne a kanmu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei cewa, bayan shahadar babban mujahidi, Isma’il Haniyyah shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Khamenei ya aike da sako.

 A sakon ta'aziyya ga al'ummar musulmi da kuma gwagwarmaya da al'ummar Palastinu, ya jaddada cewa: Da wannan mataki ne gwamnatin sahyoniyawan mai laifi  ta shirya wa kanta hukunci mai tsauri, kuma muna dauka a matsayin hakkinmu na neman fansar jinin wannan babban shahidi wanda ya yi shahada a yankin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Nassin sakon Jagoran juyin juya halin Musulunci shi ne kamar haka;

 

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai

Mu ga Allah mke kuma mu gare shi za mu koma

Ya ku al'ummar Iran!

Jarumi kuma fitaccen jagoran mujahidan Falasdinu, Isma'il Haniyeh, ya koma ga  Allah ne a daren jiya, inda ya jajanta ma babbar kungiyar gwagwarmaya kan aikin  Gwamnatin sahyoniya mai laifi da ta'addanci ta yi sanadin shahadar babban bakonmu a cikin gidanmu tare da sanya mu cikin bakin ciki, amma kuma ta shirya wa kanta hukunci mai tsanani.

Shahid Haniyyah ya dauki rayuwarsa mai daraja tsawon shekaru a fagen yaki mai daraja kuma ya shirya ya yi shahada ya sadaukar da ‘ya’yansa da iyalansa ta wannan hanyar. Ba ya tsoron zama shahidi a tafarkin Allah da kubutar da bayin Allah, amma muna ganin hakkinmu ne mu nemi daukar fansa kan jininsa a cikin wannan lamari mai daci da tsanani da ya faru a yankin Jamhuriyar Musulunci.

Ina mika ta'aziyyata ga al'ummar musulmi, ga bangaren gwagwarmaya, al'ummar Palastinu masu jaruntaka abin alfahari, musamman ma iyalai da dangin Shahid Haniyyah, da daya abokin tafiyarsa da suka yi shahada tare da shi, ina kuma yi musu addu'ar Allah ya daukaka matsayinsu a wajensa.

 

Sayyid Ali Khamenei

 

31 Yuli 2024

 

 

4229285

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Sunana Ibrahim Dabo kano Nigeria
0
0
ina farin cikinda wannan sashin hausa na iqna saboda inasamun labaranda inba awajankuba babu indazan sameshi inasamun labari na gaskiya da gaskiya dan haka nake kokari nasaka mutane layinku na labarai dan dayawa wasu basusan yadda zasu samekuba sai wanda (Allah) yanufa da samunku Nagode sosai Masha Allah danhaka ina sanar daku cewa idanda wani aiki ko rahoto na neman labarai na yau dakullun kutuntubeni zanbada gudun mawata (insha Allahu) Nagode maassalam daga usman Ibrahim Dabo
captcha